Shugabannin NNPP Sun Koma APC a Karamar Hukumar Kunchi, Kano
DSP Sanata Barau I. Jibrin CFR ya karɓi shugabannin matasa na jam’iyyar New Nigeria People's Party (NNPP) tare da daruruwan magoya baya daga ƙananan hukumomin Kunchi na yankin Kano North zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC). A yayin taron da aka gudanar a gidansa a ƙarshen mako, jagororin NNPP waɗanda suka haɗa da Hon. Shehu Usman Kuku daga Gwarmai Ward, Hon. Habibu Hassan (Ɗantala) daga Shamakawa Ward, da Hon. Sunusi Haruna Gidangoga daga Garin-Sheme Ward, sun bayyana ficewarsu daga NNPP tare da komawa APC. Sanata Barau Jibrin tare da manyan jagororin jam’iyyar APC sun tarbe su cikin farin ciki, inda sabbin mambobin suka bayyana cewa sun koma APC ne sakamakon kyawawan ayyuka da tsare-tsaren da Sanata Barau ke yi wa al’umma da ƙasa baki ɗaya. Sanata Barau ya yaba da matakin da suka ɗauka na komawa babbar jam’iyya a nahiyar Afirka, yana mai cewa APC na da damar da za ta bai wa kowane ɗan ƙasa damar ba da gudunmawa wajen ci gaban Najeriya. “A matsayinmu na jam’iyyar da ke da hangen nesa, za mu ci gaba da tarbar duk wanda ke da kyakkyawar manufa da burin ganin an kai ƙasarmu matakin ci gaba,” in ji Sanata Barau. Ya ƙara da cewa APC na maraba da duk wanda ke da muradin inganta rayuwar ‘yan ƙasa ta hanyar kyakkyawan shugabanci da ingantattun manufofi.
2/4/20251 min read

