Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Jamhuriyar Tarayyar Najeriya

DSP SANATA BARAU I. JIBRIN CFR ZAI BADA TALLAFIN KARATU GA DALIBAI 1,000 A KANO TA TSAKIYA DA KANO TA KUDU, YAYIN DA AKA KIRKIRO CIBIYOYIN KARATU NA FUDMA A MADOBI, RANO, GAYA DA SAURAN KANANAN HUKUMOMI

A ci gaba da kokari sa na samar da ilimin jami’a a dukkan kananan hukumomin jihar Kano guda 44, na kammala shirin kafa cibiyoyin karatu na jami’ar Federal University, Dutsin-Ma (FUDMA), jihar Katsina, a Kano ta tsakiya da Kano ta kudu ta hannun gidauniyata, B.I.J Foundation. A shekarar da ta gabata, na kafa cibiyoyin karatu guda hudu a kananan hukumomin Gwarzo, Danbatta, Dawakin Tofa, da Gabasawa, duk a yankin Kano ta Arewa. A karkashin wannan shiri, sama da matasa 1,000 na karatu a fannoni daban-daban na digiri. A yau, don tabbatar da cewa kowane bangare na jihar mu ya ci moriyar ilimi, na kammala tattaunawa da jami’ar FUDMA domin kafa sabbin cibiyoyi guda bakwai (7) a yankunan Kano Central da Kano South. Wadannan cibiyoyin za a kafa su a cikin kananan hukumomin Madobi, Kiru, Tudun Wada, Rano, Gaya, Dawakin Kudu, da Minjibir. Kamar yadda aka yi a Kano North, wadannan cibiyoyi za su bayar da damar karatun digiri da difloma domin bunkasa harkar ilimi a Kano. Domin farawa, zan bayar da tallafin karatu ga dalibai 1,000 daga Kano ta tsakiya da Kano ta Kudu domin su yi karatu a fannoni da suka shafi ICT a cibiyoyin karatun FUDMA. Ilimi shi ne ginshikin ci gaban kowace al’umma. Saboda haka, zan ci gaba da kokari wajen samar da ingantaccen ilimi ga mutanenmu a fadin kananan hukumomi guda 44 na Kano. DSP Sanata Barau I. Jibrin CFR

2/3/20251 min read