DSP SANATA BARAU I. JIBRIN CFR YA KARBI BAKUNCIN SHUGABANNIN DALIBAN NAJERIYA DAGA JIHAR KANO (NAKSS) A ZAUREN MAJALISAR DOKOKI TA KASA
A yau na karɓi wata tawaga daga shugabannin ƙungiyar National Association of Kano State Students (NAKSS) a harabar Majalisar Dokoki ta Kasa da ke Abuja. Tare da ni wajen tarbar shugabannin daliban akwai abokan aikina, Sanata Aminu Iya Abbas (Adamawa Central) da Sanata Adamu Lawal Usman (Kaduna Central), da kuma Manajan Daraktan/Hukumar Raya Arewa Maso Yamma (North West Development Commission - NWDC), Farfesa Abdullahi Shehu Ma'aji. Shugabannin daliban sun samu jagorancin Sakataren ƙungiyar, Comrade Sabiu Rabilu Kabo, tare da Shugaban Majalisar Dalibai, Muhammad Babangida Jibrin. Sun nuna matuƙar godiyarsu ga gudunmawar da nake bayarwa a fannin ilimi, musamman tallafin da nake bai wa dalibai a matakin gaba da sakandare da kuma matakin boko na asali. Sun jinjina wa shirina na bada tallafin karatu, wanda suka ce ya taimaka matuƙa ga ɗalibai a faɗin jihar Kano. Na gode musu bisa wannan ziyarar, tare da tabbatar musu da cewa zan ci gaba da ƙoƙari na domin samar da ingantaccen ilimi ga dukkan ‘yan kasa. Abin da muke buƙata a ƙasar nan a halin yanzu shi ne inganta rayuwar jama’a ta hanyar samar da ilimi mai nagarta da kuma ƙwarewa ga matasanmu. Idan har ba mu zuba jari a ilimin matasa ba, toh makomar ƙasar mu tana cikin haɗari. Ba na kallon siyasa idan ana batun tallafawa matasa, domin mu ne ke da alhakin gina su domin kyautata makomar Najeriya. Zan ci gaba da tallafa wa dalibai da matasa ta hanyar bayar da tallafin karatu, samar da kayayyakin koyo da kuma duk wani shiri da zai sauƙaƙa musu samun ilimi mai nagarta. Na sha alwashin ci gaba da ba da gudunmawa domin ciyar da matasa gaba, tare da ba su horo da jagoranci mai kyau, domin su zama ginshikin ci gaban ƙasar nan. DSP Sanata Barau I. Jibrin CFR
2/5/20251 min read




